Jam’iyyar NNPP Ta Shirya Zanga-Zanga Kan A Kori CP Kano Daga Mukaminsa

Alfijr ta rawaito jam’iyar NNPP, ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin nuna adawa da kamawa da tsare wasu manyan mambobinta sama da 100.

Jam’iyyar ta ce muddin ba a cire CP ba, aka kuma hukunta shi kan rashin da’a da ya yi, za a ci gaba da zanga-zangar.

Da yake jawabi a madadin jam’iyyar NNPP a Kano ranar Lahadi, dan takarar Sanatan Kano ta Arewa a majalisar dattawa, Baffa Bichi, ya yi zargin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda yana hada baki da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki domin murkushe jam’iyyar NNPP. a Zaben gwamnan jihar a ranar 15 ga Maris.

Baffa Bichi ya yi zargin cewa kwamishinan ‘yan sandan tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar na shirin kame wasu ‘ya’yan su gabanin zaben.

A cewarsa, gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta umurci shugabannin kananan hukumomi da su fitar da jerin sunayen duk wasu muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP a yankunansu, inda ya yi zargin cewa jam’iyyar na sane da cewa “an ba da jerin sunayen ga CP, kuma tuni ya ba da umurni ga DPOs za su fara aiki.”

“Sama da mambobinmu dari ya zuwa yanzu an kama su ba bisa ka’ida ba kuma ana tsare da su a hedikwatar ‘yan sanda.

Muna kuma sane da cewa dukkan ‘yan takararmu na Sanata, da ‘yan takarar Majalisar Wakilai da mafi rinjayen ‘yan takarar Majalisar Jiharmu da kuma Shugaban Jam’iyyarmu da jiga-jigan jam’iyyar duk suna cikin jerin lissafin CP da Gwamna Ganduje,” inji shi.

Bichi ya kuma yi zargin cewa kwamishinan ‘yan sandan yana aiki tare da babban mai shari’a na jihar domin gurfanar da duk ‘yan jam’iyyar NNPP da ke hannunsu na yunkurin kisan kai.

“Wannan mugunta ce, kuma Wannan zaluncin ba shi da fahimta kamar abin zargi.

“Har ila yau, CP ya umurci duk DPO da kada su karbi duk wata takardar korafi daga jam’iyyarmu.

Duk korafe-korafen da muka rubuta zuwa ga CP da duk DPO ba a yi aiki da su ba, yayin da duk wani koke-koke daga jam’iyyar APC, CP ne ya dauki matakin da gaggawa,” inji shi.

Don haka jam’iyyar adawa ta ba da wa’adin sa’o’i 24 na sakin ‘yan kungiyar da ake tsare da su, ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sa baki a yunkurin da ake yi na dakile cin zarafin ‘ya’yanta da shugabanninta, idan ba haka ba, za ta gudanar da zanga-zangar lumana a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar da ya gaggauta ɗauke Mista Daura daga Kano domin gudanar da babban zabe.

“Muna so mu bayyana babu shakka cewa jam’iyyar NNPP tana ba duk hukumomin da abin ya shafa wa’adin sa’o’i 24 da su saki dukkan mambobinmu, su kuma daina tsangwamarsu da shugabanninmu, tare da umurtar rundunar ‘yan sandan Kano da ta daina yi wa jam’iyyar APC yakin neman zabe.

“A karshen wa’adin sa’o’i 24, za mu jagoranci dukkan mambobinmu wajen gudanar da zanga-zangar lumana a dukkanin kananan hukumomin jihar 44.

Da wannan ne muka sanar da ‘yan sanda da DSS da su ba da kariya ga zanga-zangar.

“Muna so mu bayyana karara cewa jam’iyyarmu da dukkan ‘yan takararta suna tunanin ficewa daga yarjejeniyar zaman lafiya da kwamitin zaman lafiya na kasa ya sanyawa hannu idan har ba a kira CP da Gwamna Ganduje da ‘yan kungiyarsu yadda ya kamata ba don ba da damar gudanar da zaman lafiya cikin lumana.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa don jin ta bakinsa, bai amsa kiran ba har ya zuwa lokacin hada rahoton.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *