APC Ta Tafka Asarar Ficewar Ƴan Majalisar Tarayya 3 A Katsina

Alfijr ta rawaito Yan Majalisar Tarayya Masu Ci Guda Uku Na Jihar Katsina Sun bar Jam’iyyar APC sun koma Jam’iyyar PDP a jiya 29-01-2023.

Sun Bayyana Ficewar tasu ne bayan sun gana da Dan takarar Shugaban Kasar Nigeria na PDP a Jihar Sokoto.

Hakan na zuwa ne karkashin jagorancin tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina wanda shima ya watsar da Jam’iyyar APC a kwanakin baya, shine ya hada su da Atiku Abubakar din a jihar Sokoto.

Daga Cikin su yan majalisar sun hada da

  1. Hon Ahmed Dayyabu Safana (Dan Majalissar tarayya mai wakiltar Safana/Danmusa/Batsari Constituency)
  2. Hon Hamza Dalhat Batagarawa (Dan majalissar tarayya mai wakiltar Batagarawa/Rimi/Charanci Constituency)
  3. Hon Salisu Iro Isansi (Dan majalissar tarayya mai wakiltar Karamar hukumar Katsina Central Constituency).

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *