Alfijr ta rawaito Babbar kotun da ke zamanta a Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa a kalla mutane hudu, ta hanyar rataya, bisa samunsu da laifin kisan kai sauran laifuka masu alaka.
Wadanda aka yanke wa hukuncin su hudu Olabisi Bashiru, mai shekaru 50; Kayode Lahadi, 27; Rashidi Waidi, 35; da Hameed Rafiu mai shekaru 33, kuma sun amsa laifin da suka aikata.
Alkalin kotun mai shari’a S. Falola, ya yanke wa mutanen hudu hukuncin kisa saboda girman laifin da suka aikata.
Lauyan jihar, Mista Dele Akintayo, ya shaida wa kotun cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2018, da misalin karfe 2:00 na rana. a unguwar Moboreja, Ikirun, Osun.
“Wadanda aka yankewa hukuncin suna dauke da muggan makamai kuma suka tsallake shingen cikin gidan mallakar kawun Victor Akinbile kuma suka shiga dakin da yake barci ta karfin tsiya.
“Sun bukaci naira miliyan 10 daga hannun Akinbile amma ya ba su Naira miliyan 3, sun kuma karbi makudan kudade daga hannun wanda abin ya shafa, inda ya yi barazanar kashe shi.
“Daga baya wadanda aka yankewa hukuncin sun yi garkuwa da Akinbile sannan suka saka shi a cikin boot din motarsa Toyota Camry sannan suka kai shi unguwar Dominion Camp, tsohon titin Iragbiji da ke kan titin Ikirun/Osogbo suka banka masa wuta da motar wanda hakan ya yi sanadin mutuwar Akinbile.
Lauyan mai shigar da kara ya ce laifin ya ci karo da dokar fashi da makami ta 2004, wanda ke da hukuncin kisa a karkashin kundin laifuffuka, Cap 34, Volume 2, Laws na 2002.
Lauyan wadanda ake tuhuma, Mista S. Ajibade da Mista Adedayo Adedeji, sun roki kotun da ta yi musu adalci tare da jin kai wajen zartar da hukunci.
A karshe dai kotu ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin kwace babur tare da farfasa kan mai gidan da dutse.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇