Wata Gobara Ta Ƙone Motar Dakon Man Fetur A Abuja,

Alfijr ta rawaito wata tankar dakon man fetur ta kone a wani gidan mai na AA Rano, daura da babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja, a ranar Lahadi.

A cewar rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a cikin wata sanarwa, jami’an kashe gobara sun isa wurin a kan lokaci domin kashe gobarar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Josephine Adeh, ta ce, “An samu gobara a gidan mai na AA Rano.

Gobarar dai ta tashi ne a lokacin da wata tankar mai ke kara ruruwa a tashar.

“Jami’an ‘yan sanda, ma’aikatan kashe gobara da sauran masu ba da agajin gaggawa sun kasance a kasa don kashe gobarar tare da tabbatar da barnar bata yi yawa ga mutane da dukiyoyi ba.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *