APP Ta Bukaci A Kama Shugaban DSS, Kan Zargin Harin Da Matarsa Ta Kaiwa Abba Kabir

Alfijr ta rawaito Jam’iyyar Action People’s Party (APP), a ranar Litinin ta bukaci a kama shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Yusuf Bichi, biyo bayan zargin da akewa matarsa na harin da aka kaiwa dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a jihar Kano, Abba Yusuf.

Shugaban jam’iyyar APP na kasa, Uche Nnadi ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Nnadi ya koka da cewa ci gaba da zama a ofishin DSS babban abin damuwa ne.

Sanarwar ta ce a cikin zarge-zargen da ake yi wa hukumar ta sirri a makonnin da suka gabata na barazana ga alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na gudanar da sahihin zabe.

Ta tuna cewa an gano wata kara a asirce a gaban wata kotun Abuja, daga karshe kuma ta ci tura, wacce hukumar DSS ta shigar tana neman a kama gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, kan zargin badakalar kudaden ta’addanci.

Sanarwar ta kuma tuno da yunkurin tsige shugaban hukumar ta INEC Farfesa Yakubu Mahmoud da ake zargin an yi masa ne domin hana amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a (BVAS) a babban zabe mai zuwa.

A cewar sanarwar, wadannan hare-haren da ba su dace ba musamman na tsare dan takarar gwamnan jihar Kano na NNPP, Abba Yusuf, bisa umarnin uwargidan shugaban DSS din Aisha, da kuma harin da aka kaiwa shugaban kungiyar Middle Belt Youth Forum, kuma dan takarar majalisar dokoki na PDP a Kogi, Godwin Meliga, ba za a bari jam’iyyun siyasa su yi watsi da su ba.

Ta kuma dage da cewa a kama shugaban DSS, Yusuf Bichi bisa zarginsa da hannu wajen kai hari da tsare dan takarar gwamnan Kano, da kuma wasu ayyukan da hukumar tsaro ta yi zargin aikata ba bisa ka’ida ba a baya-bayan nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *