EFCC Ta Saka Kadarorin Wasu Manyan Kasar Nan A Kasuwa


Alfijr ta rawaito hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta sanar da yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga hannun ’yan siyasa da ’yan kasuwa ga ’yan Najeriya masu bukatar saya.

EFFC ta ce kadarorin na jibge ne a Jihohin Lagos da Ribas da Abuja da Anambra da Gombe da Ebonyi da Kaduna da Delta da Edo daKwara da Kuros Riba da Osun da kuma Oyo.

kadarorin da aka fitar har da na tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, wadanda hukumar ta ce an mallake su ta haramtacciyar hanya.

Sanarwar da hukumar ta wallafa ranar Asabar, ta ce daidaikun mutane da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ke son sayen kayan da aka yi gwanjon dole ne su kasance ba su da wani tabon hukuma a tare da su ko dauri.

Sanarwar ta kara da cewa ga masu bukatar sayen kadarorin, za su iya cike fom din neman saye da za a iya samu a shafin hukumar na www.efcc.gov.ng, kafin daga bisani a gayyace su don ganin kadarorin da ido.

Kadarorin da aka yi gwanjon nasu sun hada da wani gida a rukunin gidaje na Heritage Court a Jihar Ribas da wani mai daki uku a rukunin gidaje da ke rukunin gidaje na Foreshore a unguwar Ekoyin Jihar Lagos fa sauran su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *