Alfijr ta rawaito A kalla mutane 11 ne ake fargabar sun mutu sakamakon wutar lantarki da aka samu a wasu yankunan Zazzau da ke Zariya a jihar Kaduna.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Gwargwaje da Kauran Juli dake kan titin Zaria zuwa Kaduna.
An dawo da wutar lantarki a cikin babban ƙarfin lantarki a yankin da misalin karfe 1 na safe, sai ya haifar da tartsatsin na’urorin lantarki.
Hakan ya yi sanadiyar kona gidan wani Injiniya Zubair Abubakar yayin da wasu gidaje ke ci gaba da tururin hayaki,” in ji wani mazaunin yankin, Aliyu Samaila.
An tattaro cewa wadanda ake fargabar sun mutu sun hada da mace mai juna biyu, jami’an lafiya, dan sanda da sauran mutane da dama duk a yankin Gwargwaje.
Misis Christy Lombo, matar dan sandan da ya rasa ranta a lamarin da ya faru a barikin ‘yan sanda na Gwargwaje, ta ce duk sun yi barci ne a lokacin da aka dawo da wutar lantarki. “Yata ta farka ta gane cewa wasu fiwus a gidan suna cikin hayaki.
Don haka sai ta tashe ni amma kafin nan mijina ya riga ya farka ya tafi ya kashe fitila daga babban wajen canjin wutar.
“Nan da nan ya gigice wutar ta jefar da shi gefe guda, daga baya muka kai shi asibiti” inji ta.
Shugaban Kamfanin Lantarki na Kaduna (KEDCO), Abdulazeez Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, “Hatsarin ya faru ne a sakamakon layukan hayatanshin da suka cinke suka fado kan kananan layikan lantarki, wanda ya haifar da samar da haduwar wutar lantarki a waje.
“Muna ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin tare da bayyana gaskiyar wannan lamari mai ban takaici.
Muna jajantawa iyalan da suka samu asara sakamakon wannan hatsarin.
Sai dai KEDCO ta yabawa mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli bisa goyon bayan da ya bayar wajen shawo kan lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇