Saudiyya Ta Baiwa Nijeriya Gurbin Alhazai Mai Tsoka A Hajjin Baɗi

Alfijr ta rawaito hukumar Kasar Saudiyya ta bai wa Nijeriya gurbin mahajjata 95,000 a hajjin shekara mai zuwa na 2023.

Wannan na zuwa ne cikin wata sanarwa da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta fitar a shafinta na Intanet a ranar Laraba.

A hajjin bana dai an samu tsaiko, inda mahajjata da dama ba su samu damar zuwa Saudiyya ba sakamakon gaza samun jirgi da suka yi, wanda hukumar ta HAHCON bayyana cewar kamfanonin jiragen Saman ne suka kasa cika alkawarin.

Wannan karon Nijeriya za ta kammala shirye-shiryenta don gudun sake aukuwar abin da ya faru a hajjin bara, in ji sanarwar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *