Bayan Bindiga Da Tankar Mai Tayi Shaguna Da Gidaje Sun Kone

Alfijr ta rawaito Wata tanka makare da man fetur ta kwace tare da afkawa kan wasu gine-gine a yankin Apata da ke birnin Ibadan, a Jihar Oyo.

Wani ganau ya ce shaguna da gidaje sun kone sakamakon gobarar da ta tashi bayan motar ta kwace a lokacin da ta fito daga yankin Titin NNPC, ta afka wa gine-ginen da ke kallon wani gidan man NNPC..

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ce an samu cunkoson ababen hawa a babbar hanyar Ibadan zuwa Ibadan, bayan faruwar lamarin da magaribar ranar Alhamis.

Lamarin  ya faru ne a daidai Mahadar Apata daura da gidan man NNPC a kan babbar hanyar.

Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin shaguna da gidajen da tankar ta yi sanadin konewarsu ba, kuma babu rahoton mutuwa ko samun rauni a sanadin lamarin.

Tuni jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Ogun suka yi wa wajen tsinke inda suka kwana suna kokarin kashe wutar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Olawale Osifeso, ya ce tuni suka tura karin jami’ansu zuwa yankin don tabbatar da doka da oda.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *