Alfijr ta rawaito hukumar kwallon kafa ta Moroko ta kai karar alkalin wasan da ya busa wasan da suka buga tsakaninsu da Faransa a wasan Daf dana karashe.
Hukumar ta Maroko ta sanar da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA cewa bata gamsu da yadda alkalin wasan yayi ba a ranar laraba.
Ta kara da cewa, Lafari Cesar Ramos dan kasar Mexico ya hana su fenareti gabanin aje hutun rabin lokaci, wadanda a maimakon haka Ramos ya ba wa Boufal katin Gargadi.
Maroko tace sunyi tsammanin fenariti ne a lokacin da Theo Hernandez ya hada jiki da Sofiane Boufal a da’ira ta sha takwas.
FMRF ta rubutawa hukumar da ta dace domin ta sake duba hukuncin alkalan wasa da ya hana tawagar Morocco fanareti biyu a wasan.
“FMRF ta kuma yi mamakin yadda mataimakin alkalin wasa na bidiyo (VAR) bai mayar da martani ga wadannan yanayi ba.”
Tsohon dan wasan Ingila Chris Sutton, wanda ya halarci gidan rediyon Burtaniya domin sharhi ya ce na zaci fenariti aka baiwa Boufal na ketar da aka yi masa, sai naga VAR ba ta yi aikin da ya dace ba.
BBC Sport
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇