Alfijr ta rawaito Jakadan Najeriya a kasar Spain, Ademola Rasaq Seriki ya rasu.
A cewar wata sanarwa ta iyali, Marigayi Ambasada ya rasu a ranar Alhamis, 15 ga Disamba, 2022, da safe a Madrid, bisa cutar Kansa.
Sanarwar ta ce; “Inna lillāhi-wa-inna-ilayhi-rājiun “Muna cikin zukata masu nauyi da matuƙar godiya ga Allah Madaukakin Sarki cewa muna sanar da mu cewa mun yi hasarar babban ubanmu, maigida, uba, kakanmu, ɗan’uwa, kawu, da amininSa.
Mai girma, Ambasada Ademola Rasaq Atanda Seriki (CON) a ranar 15 ga Disamba, 2022.
“Ya rasu cikin lumana tare da iyalansa a Madrid, Spain,” sanarwar mai dauke da sa hannun ‘Ya’yan sa.
An haife shi a ranar 30 ga Nuwamba 1959, Ademola ɗan siyasa ne, malami, ɗan kasuwa, kuma mai kula da al’umma. Seriki ya rike mukamin karamin ministan tsaro tsakanin 2008 zuwa 2009.
Ayyukansa sun hada da kula da hukumar fansho ta soja, domin cimma manufofin da gwamnatin tarayya ta gindaya.
Shi ma tare da Ministan Tsaro, ya yi aiki don tsarawa da aiwatar da manufofi a cikin tsarin da aka ba shi.
A shekarar 2011, Seriki ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar Action Congress of Nigeria wadda bayan hadewar ta ya zama jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A farkon shekarar 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Seriki a matsayin jakadan Najeriya a kasar Spain.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇