Alfijr ta rawaito majalisar yakin neman zaben Kwankwasiyya ta amince da nadin tsohon shugaban hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin daraktan leken asiri da dabaru na majalisar yakin neman zaben.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin Majalisar Yakin Neman Zaben Gwamna na NNPP necya bayyana haka.
Muhuyi Magaji yana takun saka tsakaninsa da gwamnatin jihar Kano a yanzu karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shi a matsayin shugaban hukumar a watan Yulin 2021.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇