Dubun Wani Likitan Ta Cika Bayan Da Ya Kashe Abokin Aikinsa, Tare Da Samunsa Da Makamai

Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama wani likita da ya kashe wanda yake karewa a wurin ibadarsa a lokacin da yake gwada layar kariyar harbin bindiga.

Likitan dan asalin jihar na daya daga cikin mutane 17 da aka kama aka kuma gabatar da su bisa laifin hada baki, kisan kai, fashi da makami, sace manyan motoci, garkuwa da mutane, da kuma mallakar makami ba bisa ka’ida ba a ‘yan kwanakin nan a jihar.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, 2022, ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ya fitar.

Sanarwar ta kama cewa, kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigogi biyu, harsashi mai rai daya, bindigogin izgili guda uku, wata motar kirar Sino mai dauke da buhunan siminti 789, wayoyin hannu, katin ATM, da sauran kayayyaki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *