
Alfijr ta rawaito Rundunar ‘yan sanda jihar Delta ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da cewa jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ne.
A cewar rundunar ‘yan sandan, wadanda ake zargin sun amince da yi wa mutane fashi a sassa daban-daban na jihar.
Bright Edafe, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce ayyukan wadanda ake zargin ne ya janyo zanga-zangar ta EndEFCC a jihar a watan Oktoba.
Wadanda ake zargin sun hada da Prince Allison, mai shekaru 29, George Onyeweagu, mai shekaru 29, Duke Okoro mai shekaru 40, Joseph Osinachi, da kuma Onyocha Sunday, mai shekaru 32.
Edafe ya bayyana cewa, wanda aka kama ya bayyana yadda suka kutsa cikin gidansa da daddare, suka yi awon gaba da shi, suka kuma karbe masa. tsabar kudi N2,500,000.
“Shida daga cikin wadanda abin ya shafa kuma sun gano su, daya kuma ya bayyana cewa ‘yan kungiyar sun kai farmaki gidansa da daddare,” in ji kakakin ‘yan sandan Delta.
“Sun samu shiga harabar gidan ne ta hanyar yi masa kofar rago, suka shiga gidansa, suka yi awon gaba da shi da karfi suka tafi da shi cikin wata farar motar kirar Toyota Hiace.”
Kuma suka karbe masa wayoyinsa da karfi, da wasu kayayyaki masu daraja na miliyan uku, naira dubu dari bakwai (N3). ,700,000), ya aika da tsabar kudi miliyan biyu, naira dubu dari biyar (N2,500,000) sannan suka ce masa za su sake kawo masa.”
A watan Oktoba ne dai wasu matasa a jihar Delta suka tare wasu hanyoyi a sassan jihar domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin kame matasa da jami’an EFCC ke yi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ