Majalisar Dattijai Ta Yi Watsi Da Zargin Badakala A NDDC

Alfijr ta rawaito Kwamitin Da’a Da Gata Na Majalisar Dattijai na binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa a Hukumar Raya Neja Delta (NDDC).

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kararrakin jama’a Sanata Ayo Akinyelure ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a zauren majalisar.

Ya ce binciken ya biyo bayan wani koke da ake zargin tsohon ministan harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio da hukumar NDDC da kin rubuta nadin wasu masu neman aiki guda bakwai daga jihar Ondo da suka gabatar da takardar neman aiki bisa ga doka kuma aka ba su wasikun aiki don yin aikin hukumar.

Sanata Akinyelure, ya ce kwamitin da’a ya wanke ministar harkokin Neja-Delta, Umana Okon Umana daga aikata ba dai-dai ba kan zargin satar ayyukan yi da cin hanci da rashawa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *