Maihifiyar Ummita Ta Musanta Kashewa Ƴar Ta Miliyan 170

Alfijr ta rawaito a zaman babbar kotun na yau Laraba, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa ɗan China da kashe tsohuwar budurwarsa Ummulkhuksum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.

Lauyan dan China ya bayyana cewa dan China har garin su, Sakoto yaje sau uku yana gaishe da iya yenta tare da yi musu kyaututtuka , sun kuma shafe shekara biyu tare da Ummita.

Anata bangaren mahaifiyar Ummita ta ce zuki ta mallece, sau daya ta san yaje Sokoto domin gaida dangin nata.

Hajiya Fatima, ta faɗa wa kotun cewa a ranar 16 ga watan Satumbar 2022 Mista Geng Quangrong ya je gidansu inda ya yi ta buga kofa, bayan da suka bude kofar a cewarta, sai ya shiga dakin Ummita ya kulle kofar, da kuma ta leka ta taga sai ta ganta cikin jini, al’amarin da yasa ta fita waje neman a kawo musu dauki.

Lauyan dan China ya tambayi Kanwar Ummita cewar ko tasan dan China ya kashe wa Ummita kudi miliyan dari da saba’in, ya ce ya kuma saka mata wani tallafi da yake bata dubu dari duk sati?

Haka kuma ya taba shirya wa Ummita bikin birthday da a kashe kudi sama da dubu dari bakwai da saba’in.

Ya kuma siya mata gwala-gwalai na sama da naira miliyan uku da dubu dari uku a watan mayu na shekarar da muke ciki.

Sai dai Kanwar Ummita tace bata san ya yiwa Ummita wadannan abubuwan ba kawai tasan ‘yan uwansu ne basa son auren Ummita da dan China.

kwamishinan Shari’a na jihar Kano Musa Abdullahi-Lawan shi ya jagoranci lauyoyin gwamnati a zaman kotun domin kare majigayiya Ummita.

Sakamakon musayar bayanai da tambayoyi da aka riƙa yi wadanda suka dauki hankali sosai, abin da yasa har hutu mai shari’a ya ta fi har sau biyu.

Alkalin babbar kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage zaman zuwa gobe da kuma jibi juma’a inda ake fatan ci gaba da sauraren shaidu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

2 Replies to “Maihifiyar Ummita Ta Musanta Kashewa Ƴar Ta Miliyan 170

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *