
Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sanda ta jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar wani mutum a yankin Girei da ke jihar Adamawa.
Bayanai sun bayyana cewa mutumin ya kashe kan sa ne saboda zargin da aka yi masa na satan kuɗi, wanda shi kuma ya sha musantawa.
Kakakin yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya ce yanzu haka hukuma ta fara bincike kan lamarin domin gano yadda mutuwar tasa ta samo asali.
A bayanin da ya yi wa BBC, SP Suleiman ya ce sun samu rahoto ne na cewar wani mutum ya rataye kan shi a dajin ƙaramar hukumar Girei.
Sai dai ya ce a lokacin da jami’an suka isa wurin, gawar ta fara ruɓewa, amma sun samu wata takarda a gefensa, inda aka rubuta sunanasa da ƙaramar hukumar da ya fito.
Ya ƙara da cewa takardar na ƙunshe da cewa an zarge shi ne da satan kuɗi naira 400 ko 40,000.
“Hakan ne ya ɓata masa rai ya ɗauki matakin da ya ɗauka.”
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ