Dan Majalisar Dokoki Ya Mutu A Taron Jam’iyyar APC A Jos

Alfijr ta rawaito sani Dan Majalisar Dokokin Jihar Lagos, Hon. Abdulsobur Olayiwola Olawale ya rasu a yau Talata.

Dan majalisar wanda aka fi sani da Omititi, marigayin yana wakiltar mazabar jihar Mushin II.

Rahotanni sun ce jigon jam’iyyar APC ya mutu a filin wasa na Rawang Pam Township da ke Jos, a ranar Talata, lokacin gangamin kaddamar da takarar Asuwaju Bola Tinubu.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa na 2023 a ranar Talata a jihar Filato. Omititi ya kasance shugaban kwamitin majalisar akan ayyuka na kananan hukumomi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

One Reply to “Dan Majalisar Dokoki Ya Mutu A Taron Jam’iyyar APC A Jos”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *