
Alfijr ta rawaito wani Miji mai suna Akpos ya kone Matarsa mai suna Risikat, har lahira.
Mijin matar ya tsere daga gidansu da ke kan titin Ayide Osolo, Divine Estate, a unguwar Ijaniki a jihar Lagos tun lokacin da lamarin ya faru.
An tattaro cewa an gwabza kazamin fada tsakanin mutanen biyu ne biyo bayan takaddamar da ta barke a tsakaninsu.
Majiyar ta kara da cewa gardamar ta kaure, Akpos saboda bacin rai ya kai ga neman mai, ya zuba wa matarsa, ya banka mata wuta.
Rahotanni sun ce wasu Samari ne suka garzaya da matar zuwa wani asibiti da ke kusa domin yi mata magani, bayan da aka sanarwa da jami’an tsaro, rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Ijanikin domin gudanar da bincike.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce Risikat ta samu munanan raunuka, inda ya ce ta rasu ne a lokacin da take jinya a asibiti.
Ya ci gaba da cewa, “An samu rahoton wata kara a ofishin ‘yan sanda na Ijanikin cewa wata mata mai suna Risikat ‘yar shekara 48 ta samu sabani da mijin nata, kuma ana cikin haka sai ya zubawa matarsa man fetur ya banka mata wuta.
“Hakan ya jawo konewar jiki sosai kuma nan take aka garzaya da ita asibiti domin yi mata magani amma ta mutu.
Ya kuma bayyana cewa ana kokarin kama mijin da ya gudu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux