Sanata Dr. Idiat Oluranti Adebule, mai wakiltar mazabar Sanatan Lagos ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya, ta rasu tana da shekaru 56, kwana guda kacal bayan gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, 2026, a wani asibiti mai zaman kansa da ke yankin GRA, Ikeja, a jihar Legas, bayan fama da rashin lafiya. Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a bayyana takamaiman dalilin rasuwarta ba.
Kafin rasuwarta, Adebule ta kasance tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas, inda ta yi aiki a karkashin tsohon Gwamna Akinwunmi Ambode daga shekarar 2015 zuwa 2019. Haka kuma, ta taba rike mukamin Kwamishiniyar Ilimi da kuma Sakatariyar gwamnatin jihar Legas.
An zabi marigayiyar a matsayin Sanatar Lagos West a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar APC, inda ta wakilci al’ummar yankin a Majalisar Dattawa ta 10. Ta kasance tana shirin sake neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2027 kafin rasuwarta.
Marigayiyar, wadda ta fito daga kabilar Awori ta jihar Legas, ta cika shekaru 56 a ranar Juma’a, 27 ga Nuwamba, inda ta wallafa sakon godiya ga Allah bisa baiwar rayuwa tare da addu’ar samun karin karfin gwiwa wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima.
Rasuwarta ta jefa al’ummar jihar Legas da masoyanta cikin alhini, musamman ganin cewa ta rasu ne kwana guda bayan murnar zagayowar ranar haihuwarta. Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya kuma bai wa iyalanta da daukacin al’ummar da ta bari hakurin jure wannan babban rashi.
📢 KU BIBIYI ALFIJIR LABARAI
Ku kasance tare da Alfijir Labarai / Alfijir News domin samun sahihan labarai, rahotanni, bincike da muhimman bayanai daga Kano, Najeriya da duniya.
📩 TUNTUƁA DA HAƊIN GWIWA
WhatsApp: +234 0701 111 3809
KIRA: +234 803 207 7835
🌐 KAFAFEFENMU
X: https://twitter.com/Musabestseller?s=09
Facebook: https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
Threads: https://www.threads.net/@alfijirlabarai
YouTube: https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
Instagram: https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
📲 WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Ilj1iz8v3sa3nBfrCz9U6f
ALFIJIR LABARAI MEDIA SERVICES
Gaskiya • Kan Lokaci • Amintacce
© 2026 Alfijir Labarai Media Services
