Gwamnatin Jihar Kano ta ware filaye ga matasa 1,000 daga kananan hukumomi 44 na jihar, a wani muhimmin shiri da aka tsara domin karfafa matasa bunkasa mallakar gidaje, samar da dukiya da kuma ba su damar samun makoma mai inganci.
Da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen rabon takardun filayen a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnati a Kano Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Farouk Umar Ibrahim, ya ce shirin ya nuna kudurin gwamnatin na samar wa matasa kadarori da damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa makomar Kano tana da alaka sosai da ci gaban matasan ta, yana mai cewa gwamnati mai hangen nesa dole ta zuba jari wajen samar wa matasa damarmaki na mallakar kadarori, gina dukiya da kuma taka rawa wajen ci gaban al’umma.
Ya ce fili na daga cikin muhimman kadarorin da mutum zai iya mallaka saboda darajarsa na karuwa, yana samar da damar tattalin arziki da kuma zama ginshikin tsaron makomar iyalai da gina dukiya mai dorewa.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba kawai filaye aka bai wa matasan ba, illa filaye ne da ke cikin tsare-tsaren gine-gine da gwamnati ta amince da su, wadanda aka tsara da tanadin hanyoyi, magudanan ruwa, makarantu, cibiyoyin lafiya, wuraren ibada, kasuwanni, wuraren shakatawa da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su dauki takardun rabon filayen a matsayin wata dama ta mutunci da tsaro, su kare filayensu, su guji sayar da su don neman riba cikin gaggawa, sannan su gina su gwargwadon karfins u.
A nasa bangaren, Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce shirin na da nufin samar wa matasa kadarorin da za su kasance ginshikin mallakar gidaje, kafa sana’o’i da samar da dukiya mai dorewa. Ya bayyana cewa gwamnatin ta tsaurara yaki da masu kwacen filaye ba bisa ka’ida ba, wato “Awan Igiya.”
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
