Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO na shekarar 2027 domin bai wa masu ruwa da tsaki damar tattaunawa kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Ma’aikatar Ilimi ta tarayya ta bayyana cewa ta janye wasiƙar da ta fitar a ranar 18 ga Yunin 2026 wadda ta sanar da ƙarin kuɗin, bayan korafe-korafe da ra’ayoyin jama’a.
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya umarci a dakatar da shirin domin tabbatar da an yi cikakken nazari tare da tattaunawa da hukumomin shirya jarabawa, ma’aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, ƙungiyoyin iyaye, ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki.
Ma’aikatar ta ce an yi tunanin ƙara kuɗin ne saboda tsadar gudanar da jarabawa da ta haɗa da sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha da kuma tabbatar da inganci.
A baya dai Gwamnatin tarayya ta amince da ƙara kuɗin rajistar WAEC da NECO daga N27,500 zuwa N50,000 daga shekarar 2027, matakin da ya fuskanci suka daga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS). Ma’aikatar ta ce sabon tsarin ba zai fara aiki ba har sai an kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
