Makwantar Rikici: Hukumar EFCC Ta Kwato Miliyan 7.2 Da ‘Yan Damfara Suka Sace A Asusun Wata Alƙaliya

FB IMG 1783161714531

Shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziki da ta’annati ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda wasu da ake zargin masu damfarar intanet (Yahoo Boys) suka sace sama da Naira miliyan 7.2 daga asusun ajiyar wata alƙaliya.

Olukoyede ya ce kuɗin da aka sace ajiyar shekaru shida ne da alƙaliyar ta tara domin biyan kuɗin karatun ɗanta. Ya bayyana cewa alƙaliyar ta kira shi da misalin ƙarfe ɗaya na dare bayan ta fara karɓar saƙonnin cire kuɗi daga asusunta.

A cewarsa, bayan alƙaliyar ta nemi taimakon EFCC, hukumar ta gaggauta fara bincike tare da samun nasarar kwato duka kuɗin kafin ƙarfe shida na yammacin wannan rana.

Shugaban EFCC yayi kira ga ‘yan Najeriya, hukumomin tsaro da ɓangaren shari’a da su haɗa kai wajen yaƙi da laifukan intanet, yana mai cewa haɗin gwiwa ne kaɗai zai kawo ƙarshen wannan barazana.

Ya kuma buƙaci a samar da sabbin dokoki da za su taimaka wajen amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) a bincike da yaƙi da aikata laifuka.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *