Ana Wata: Takarar Obi da Kwankwaso a 2027, na fuskantar turjiya a Arewacin Najeriya

FB IMG 1778388013088

Rahotanni da jaridar Punch ta tattaro sun nuna cewa takarar shugaban ƙasa ta haɗakar ɗan takarar NDC, Peter Obi da abokin takararsa Rabiu Musa Kwankwaso, na fuskantar turjiya daga wasu jagororin siyasa da masu kaɗa ƙuri’a a Arewacin Najeriya.

Wasu shugabannin Arewa sun bayyana cewa jam’iyyar NDC har yanzu ba ta samu karɓuwa sosai a tsakanin al’ummar yankin ba, yayin da ake yaɗa saƙonnin siyasa a wasu kafafen sada zumunta da ke ƙoƙarin nuna haɗakar Obi da Kwankwaso a matsayin wadda ba ta dace da muradun Arewa ba.

Mai magana da yawun Arewa Consultative Forum, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya ce har yanzu yawancin masu zaɓe a Arewa ba su san NDC sosai ba.

Ya bayyana cewa duk da shaharar wasu fitattun ‘yan siyasa a kafafen yaɗa labarai, hakan ba ya nufin suna da cikakken goyon bayan jama’a. Ya kuma nuna shakku kan ko Kwankwaso zai iya riƙe tasirinsa a Kano kamar yadda ya yi a zaɓen 2023.

A cewarsa, yawancin ‘yan Arewa sun fara gajiya da siyasar ƙabila, addini da yanki, suna neman shugabanni masu kawo mafita ga matsalolinsu na rayuwa.

Shugaban Arewa Youth Consultative Council, Zaid Ayuba, ya ce Obi bai samu karɓuwa a Arewa ba saboda abin da ya kira alaƙarsa da masu rajin kafa ƙasar Biafra.

Ya ce akwai buƙatar Obi ya yi karin bayani kan matsayinsa game da ƙungiyar Indigenous People of Biafra idan yana son samun amincewar masu zaɓe daga Arewa.

Wani farfesan ilimin siyasa daga Sokoto ya bayyana cewa NDC ba ta da ƙarfi a jihohi da dama kamar Kaduna, Katsina, Jigawa, Gombe, Niger, Taraba, Zamfara da wasu jihohin Arewa.

Ya ce matsalar ba wai rashin karɓuwa ba ce kawai, illa kasancewar jam’iyyar sabuwa ce kuma ba ta da cikakken tsari kamar APC, PDP ko ADC.

A wata sanarwa da Northern Youth Assembly ta fitar, an zargi Kwankwaso da watsi da muradun Arewa saboda haɗin gwiwarsa da Obi.

Kungiyar ta ce Kwankwaso ya kauce daga manufofin da suka gina tafiyar Kwankwasiyya, tana mai cewa ya kamata shugabannin Arewa su fifita ci gaban yankin a duk wata lissafin siyasa.

Sai dai shugabannin NDC a wasu jihohin Arewa sun musanta waɗannan ikirari.

Shugaban NDC na jihar Borno, Haruna Amuda, ya ce dubban mutane na ci gaba da shiga jam’iyyar daga wasu jam’iyyu, musamman ADC.

A Jigawa kuwa, wani jigo a jam’iyyar, Abdulrazak Birnin-Kudu, ya ce sun kafa masu gudanarwa a dukkan ƙananan hukumomin jihar tare da ci gaba da wayar da kan matasa.

Daraktan yankin Arewa na Civil Liberty Organisation, Steve Aluko-Daniel, ya ce NDC na samun karɓuwa sosai a Arewa saboda rashin wata ƙungiya guda da ke jagorantar siyasar yankin bayan zamanin Muhammadu Buhari.

Ya ce mutane da dama suna komawa NDC ne saboda tasirin Obi da Kwankwaso, yana mai cewa idan aka gudanar da sahihin zaɓe a yanzu, jam’iyyar za ta iya yin tasiri sosai a Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.

Rahoton ya nuna cewa yayin da wasu kungiyoyi da shugabannin Arewa ke nuna shakku kan karɓuwar haɗakar Obi da Kwankwaso a yankin, shugabannin NDC da wasu masu sharhi na siyasa suna cewa jam’iyyar na ci gaba da samun karɓuwa tare da gina tsari a jihohin Arewa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Duk da haka, karɓuwar jam’iyyar da tasirin haɗakar Obi-Kwankwaso a Arewa na ci gaba da zama muhimmin batu a siyasar Najeriya.

IJaridar Punch/Fassarar DCL Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *