Masallata da dama, sun rasa ransu wasu kuma sun jikkata yayin sallar magariba a Maiduguri

FB IMG 1766675358520

Daga Salma Muhammad Jega

An rawaito cewa masu ibada sun rasa rayukansu wasu sun jikkata bayan wani ɗan kunar bakin wake ya tayar da bam a masallacin Juma’a na Gambarou da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Alfijir Labarai ta rawaito wasu daga cikin masu ibadar da suka tsira daga harin sun ce maharan sun shiga masallacin a ɓoye, sannan suka tayar da bam ɗin ne a lokacin sallar Magariba tare da jama’a.

“Ɗan kunar bakin waken ya tayar da bam ɗin ne a raka’a ta farko ta sallar Magariba. Mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun jikkata da raunuka iri-iri,” in ji wani da ya tsira.

Sai dai ba a samu wanda ya ɗauki alhakin harin nan take ba, amma ana zargin ƙungiyar Boko Haram da aikatawa, kasancewar ta ƙaddamar da hare-haren kunar bakin wake da dama a yankin cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *