An ƙara tsaurara matakan tsaro a gidan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ke Daura, garinsa na asali a Jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne yayin da ake sa ran za a sauke gawar marigayi shugaban ƙasar daga London nan ba da jimawa ba.
Shugaba Bola Tinubu, wanda zai karɓi gawar da kansa a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, ya riga ya aika Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatansa, zuwa Burtaniya domin su raka gawar zuwa gida.
Lokacin da jaridar Daily Trust ta ziyarci gidan Buhari da ke Daura a yau Talata, jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da sojojin Najeriya sun kasance tsaye a bakin ƙofar shiga gidan.
‘Yan sanda da jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) kuwa suna tsaye a wurare masu muhimmanci a cikin unguwar.
Wasu majiyoyi da daga gidan sun tabbatar wa Daily Trust cewa an riga an fara aikin haƙa kabarin.
Tun da farko, Daily Trust ta tattaro cewa an ware wani ɓangare na gidan marigayi shugaban domin binne shi a ciki.
Wani wanda ya ƙi bayyana sunansa, ya ce wurin da za a binne shi za a zagaye shi da katanga.
A cewar Garba Shehu, mai magana da yawun marigayi shugaban, ana sa ran jirgin da ke ɗauke da gawar zai sauka tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na rana a yau Talata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD