NIMC ta magantu akan matsalar Suwafin din layika da ake cikinsu a yanzu

IMG 115444 12725 1752317751387

Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) a ranar Juma’a 11 ga Yuli, ta bayyana cewa, shafinta na tantancewa da tabbatar da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) na aiki yadda ya kamata, duk da korafe-korafen da jama’a da kamfanonin sadarwa ke yi kan tsaikon da suke fuskanta wajen samun sabis.

A cikin ‘yan makonnin nan, jama’a da dama a Najeriya sun koka da yadda suka kasa dawo da lambobin wayarsu ko kammala wasu sabis da suka shafi SIM, sakamakon abin da suka bayyana a matsayin tsaiko mai tsawo daga shafin tantancewar NIN na NIMC.

A Najeriya, domin samun sabis na sauya katin SIM, sai an tabbatar da asalin mai layin, wanda ake yi ta hanyar tabbatar da lambar NIN da lambar wayar — domin kare jama’a daga zamba da satar layi.

Wannan tsaiko, wanda ya fara tun makon da ya gabata, ya ci gaba har zuwa karshen mako duk da sanarwar da NIMC ta bayar cewa ta dawo da ayyukanta yadda ya kamata.

A martani, kamfanin Airtel Nigeria ya rubuta a shafinsa na X game da yawan korafe korafe daga jama’a ya ce: “Don Allah ku sani cewa shafin NIN a halin yanzu ba ya aiki. Wannan ne yasa ba ma samun damar gyara mu ku layukan da kuke bukata. Kuma muna bakin cikin wannan jinkiri.”

Daga baya, kamfanin ya sake wallafa sako yana cewa har yanzu ba a gyara matsalar ba, amma ana aiki domin dawo da shafin.

Sai dai NIMC ta musanta cewa matsalar daga gareta ne. Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na hukumar, Kayode Adegoke, ya shaidawa jaridar Saturday PUNCH cewa shafin na aiki yadda ya kamata, yana mai cewa matsalar na iya kasancewa daga bangaren kamfanonin sadarwa.

“Shafinmu yana aiki yadda ya kamata. Shi ne kuma wasu hukumomin gwamnati ke amfani da shi don tabbatar da bayanai da yin gyara,” in ji Adegoke.

A makon da ya gabata, hukumar ta sanar da kammala aikin gyara na fasaha da dawo da cikakken sabis a fadin kasar.

“NIMC na sanar da al’umma cewa aikin gyaran fasaha da aka gudanar ya kammala, kuma dukkan ayyuka sun dawo yadda suka kamata,” in ji hukumar a wata sanarwa.

Hukumar ta bukaci ‘yan kasa da ke son yin rijistar NIN su ziyarci shafinta domin gano cibiyar rijista mafi kusa da su.

NIMC ta kara da cewa jama’a za su iya saukar da manhajarta mai suna NameAuth (oath.app) daga Google Play Store ko Apple App Store domin tabbatar da sahihancin lambar NIN dinsu.

Sai dai duk da wadannan tabbacin, jama’a na ci gaba da fuskantar matsaloli wajen samun sabis na sadarwa da suka shafi NIN, musamman ma batun sauya katin SIM.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *