Tinubu ya caccaki El-Rufai, Atiku, Amaechi da wasu da ke shirin hadaka domin kada shi

FB IMG 1723115651747

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki wadanda ke goyon bayan wata hadakar siyasa da ke neman hana shi sake cin zabe a 2027, inda ya bayyana su a matsayin ‘yan gudun hijira na siyasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin dayake kaddamar da wasu ayyuka a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule ne ya gudanar da ayyukan, wanda shugaban ya yaba da yadda ya ba da fifiko ga walwala da ci gaban al’ummarsa.

Da yake yaba wa ayyukan gwamnan, Tinubu ya ce: “Sule yana ayyuka masu kyau saboda haka Bola Tinubu yana jin dadi.”

Ya kuma yaba da yadda Sule ke yin amfani da dukiyar jihar tare da yin alkawarin ci gaba da baiwa gwamnatin tarayya goyon baya ga Nasarawa.

“Na ga aiki tukuru yana fitowa daga A.A Sule, wanda ya kuduri aniyar yin amfani da albarkatun da yake da shi don amfanawa da ci gaban jihar Nasarawa,” in ji Tinubu.

Da yake jawabi ga gamayyar kungiyoyin adawa da aka rawaito dasuka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, Tinubu ya yi watsi da kawancen a matsayin wani yunkuri na siyasa mara tasiri..

Ya bayyana cewa ba zai nade hannayen sa a shirin da ‘yan adawa ke shirin tsige shi.

Gabanin zaben shugaban kasa na 2027, jiga-jigan ‘yan adawa, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; takwaransa na jam’iyyar Labour, Peter Obi; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Rahotanni sun bayyana cewa, da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, na tattaunawa domin kulla kawance da nufin kakkabe jam’iyyar APC mai mulki.

Yayin gabatar da tambayoyi a gidan talabijin na Channels Television’s Politics A Yau, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasa, Paul Ibe, ya tabbatar da rade-radin da ake yi na shirin hadakar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *