Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi gargaɗi cewa Iran za ta mayar da mummunan martani idan Amurka ta ɗauki matakin soji kan ƙasar.
Cikin wata sanarwa da jagoran ya fitar, aka kuma karanta a gidan talbijin na ƙasar, Ayatolla ya ce Iran ba za ta lamunci hari daga Amurka ba.
“Idan Amurka ta yi amfani da karfin soja, za ta fuskanci lahani da ba za a iya gyarawa ba.”
“Mutane masu hikima waɗanda suka san Iran da mutanenta da tarihinta, (sun san cewa) ba a yi musu barazana, domin Iraniyawa ba mutane ne da ke miƙa wuya ba,” in ji Khamenei a cikin sanarwar.
BBC
Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD