Yayin da yanayin zafi ke ƙaruwa a yankin, Saudiyya ta kunna tsarin sanyaya waje mafi girma a duniya a Masallacin Harami na Makkah da Masallacin Annabi a Madina domin sauƙaƙa aikin Hajji ga mahajjata sama da miliyan ɗaya da suka fara ibadunsu a ranar Laraba.
Ana sa ran yanayin zafi zai haura digiri 40 a ma’aunin salshiyas.
A cewar jaridar Saudi Gazette, wannan tsarin sanyaya wajen yana da ƙarfin ton 155,000 gaba ɗaya.
Tsarin sanyaya waje na Masallacin Harami, yana dogara ne a kan tasoshi biyu: Tashar Al-Shamiya mai ƙarfin ton 120,000 da Tashar Ajyad mai ƙarfin ton 35,000, kamar yadda jaridar Saudiyya ta bayyana.
Dukkanin tasoshin suna sanyaya dukkanin kewayen masallacin, ciki har da wuraren da aka faɗaɗa da kuma wasu tsofaffin sassan masallacin da suka samo asali tun karni na 16, suna tabbatar da cewa mahajjata suna jin yanayi mai sanyi-sanyi daga digiri 22° zuwa 24° na salshiyas.
Domin tabbatar da samun iska mai inganci, tsarin yana aiki da fasahar da take zuƙe kashi 95 cikin 100 na gurɓatacciyar iska mai iya watsa cututtuka. Hakan zai tabbatar da samar da kyakkyawan muhalli mai tsabta da lafiya ga mahajjata, musamman a lokacin zafi mai tsanani.
Hukumar Haramin za ta tabbatar da dukkanin ayyukan gyara, ciki har da maye gurbin muhimman sassa da tabbatar da tsaron wuraren aiki, da kuma sarrafa albarkatu yadda ya kamata domin biyan buƙatun mahajjata .
An kafa tsauraran dokoki a kan baƙi marasa izinin shiga Makkah domin hana cunkoson jama’a. A bara, hukumomin Saudiyya sun ba da rahoton mutuwar mahajjata 1,300 yayin da yanayin zafi ya kai digiri 50 a ma’aunin salshiyas.
Da yawa daga cikinsu ba su yi rijista ba kuma ba su da damar shiga tantunan masu samar da sanyi da kuma motocin bas-bas.
A cewar The National, Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya ya ruwaito cewa “wannan ƙoƙarin wani ɓangare ne na hangen nesa mai zurfi da nufin inganta ƙwarewar mahajjata da samar da mafi girman matakan jin daɗi da kwanciyar hankali yayin gudanar da ibada, musamman duba da yanayin zafi mai tsanani.”
Hukumomin Saudiyya sun kuma roƙi mahajjata da su zauna cikin tantunansu na tsawon sa’o’i a lokacin ƙololuwar aikin Hajjin wannan makon, suna nuna yanayin zafi mai tsanani.
A cewar wani rahoto a kafafen watsa labarai na Saudiyya, Ministan Hajji Tawfiq al-Rabiah ya nemi mahajjata da su guji fita daga tantunansu tsakanin ƙarfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma a ranar Alhamis.
“Ranar Arafa” ita ce ranar ibada mafi nuna ƙololuwar Aikin Hajji, lokacin da mahajjata ke hawa Dutsen Arafa a wajen birnin Makkah.
A nan, mahajjata suna taruwa a kan tsaunin mai tsawon mita 70 (ƙafa 230) da filin da ke kewaye da shi na sa’o’i suna addu’a da karatun Ƙur’ani, har zuwa maraice.
Babu inuwa sosai a kan Dutsen Arafat, lamarin da kan sa mahajjata su zauna a ƙarƙashin rana mai tsanani tsawon tsawon sa’o’i.
“Muna gargadi a kan hawa duwatsu ko wurare masu tsayi a Ranar Arafat, domin hakan yana haifar da gajiya mai tsanani da kuma ƙara haɗarin kamuwa da zafin rana,” in ji ma’aikatar lafiya a cikin wata sanarwa daban da aka wallafa a kafafen watsa labarai na Saudiyya.
Ana hasashen yanayin zafi na bana zai haura digiri 40 yayin da aka fara ɗaya daga cikin manyan tarukan addini na duniya, wanda ke haɗa masu ibada daga ko ina cikin duniya a ranar Laraba.
Hukumomi sun ƙara matakan rage zafi da fatan kauce wa maimaita abin da ya faru a Hajjin bara, inda mahajjata 1,301 suka rasu yayin da yanayin zafi ya kai digiri 51.8°.
A bana, hukumomi sun tura fiye da hukumomin gwamnati 40 da jami’ai 250,000, suna ninka ƙoƙarinsu a kan cututtukan da suka shafi zafi bayan mummunan zafin rana na 2024.
An faɗaɗa wuraren inuwa da mita murabba’i 50,000 (kadada 12), an ƙara yawan likitoci, kuma za a tura fiye da na’urorin sanyaya waje 400, in ji ministan Hajji ga AFP makon da ya gabata.
Tun daga ranar Lahadi, mahajjata fiye da miliyan 1.4 sun isa Saudiyya domin Aikin Hajji, a cewar hukumomi.
TRT Hausa
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN