NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

FB IMG 1747675769083

Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu da kuma jam’iyya mai mulki ta APC dangane da wasu kalaman suka da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi a kwanakin baya.

Jam’iyyar ta gargadi Kwankwaso da kada ya kara amfani da sunanta wajen sukar Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC, tana mai cewa tsohon gwamnan jihar Kano an kore shi daga NNPP tuni.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na kasa na NNPP, Dakta Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a Legas, jam’iyyar ta nesanta kanta daga kalaman Kwankwaso, inda ta bayyana cewa an katse duk wata alaka tsakaninta da Kwankwaso da kuma kungiyar Kwankwasiyya da yake jagoranta.

“Muna neman afuwa  ga Shugaban kasa Bola Tinubu da dukan iyalan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje, bisa cin mutunci da kalaman batanci da Kwankwaso ya furta,” in ji Olaposi.

“Kwankwaso ya daina bayyana kansa a matsayin dan jam’iyyar NNPP da kuma amfani da sunanta wajen kai hari ga jam’iyyar APC da fadar shugaban kasa,” in ji shi. “An kore shi tun tuni, kuma maimakon ya zargi wasu, ya duba kansa idan mabiyansa suna komawa APC.”

Daily Nigerian

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *