Ana zarginsa da hannu wajen taimakawa ta’addanci da sauran laifuka a yankin arewacin Najeriya.
Alfijir labarai ta ruwaito Bashir Hadeija, na hannun daman karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, an kama shi ne bisa zarginsa da bindigu da safarar manyan muggan makamai, biyo bayan hadaddiyar kungiyar ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya, kamar yadda Peoples Gazette ta ruwaito.
Hadeija, wanda ya kasance mataimaki na musamman ga matawallen lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara, an kama shi ne a karshen mako kan tuhumarsa da laifin karkatar da kudade da sauran laifuffukan da suka shafi gwamnati.
Wanda ake zargin a halin yanzu yana hannun jami’an tsaro domin fuskantar tambayoyi kan zarginsa da aikata laifuka da dama, ana kuma zarginsa da hannu wajen taimakawa ta’addanci da sauran laifuka a yankin arewacin kasarnan.
Jim kadan bayan kama shi, faifan bidiyo sun nuna Mista Hadejia yana baje kolin sandunan Zinare da aka rubuta da sunan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi.
Jaridar Gazette ta ce ta kasa samun martanin ‘yan sanda da masu magana da yawun DSS kan kamun da aka yi masa, sai dai majiyoyin tsaro daban-daban na jami’an leken asirin da suka tabbatar da kama shi, sun ce har yanzu yana tsare kuma ana yi masa tambayoyi.
Sai dai kuma, kamen Bashir na haifar da martani dangane da alaka da manyan da kuma fitattun ‘yan siyasa ciki har da Matawalle, a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a yankin arewa maso gabashin kasarnan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj