Ƙungiyar CNPP ta Buƙaci A dakatar da Mele Kyari, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL).
Alfijir labarai ta ruwaito cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun mataimakin kakakinta James Ezema, Kungiyar CNPP ta kuma bukaci a gudanar da bincike kan zarge-zargen badakalar tallafin man fetur, da shigo da man fetur marasa inganci, da kuma rashin gudanar da aikin matatar mai na Fatakwal.
CNPP ta bukaci hukumomi da su yi wa NNPCL hisabi ta hanyar dakatar da Mele Kyari nan take tare da gudanar da bincike mai zaman kansa kan badakalar tallafin da sauran zarge-zarge da ake yi a sassan mai na Najeriya domin kare tattalin arzikin kasar da rage radadin wahala.
Kungiyar ta soki yadda ake ci gaba da samun karin farashin man fetur daga Naira 167 zuwa kusan Naira 700 a kowace lita, bisa zargin cire tallafin man fetur, inda ta yi nuni da cewa “man fetur ya yi karanci, yana kara jawo wa ‘yan kasa wahala.”
Da yake jawabi a kan zargin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi, wanda ya yi ikirarin cewa “mutane a NNPCPL ba sa son a kawo karshen badakalar kudaden tallafin,” jam’iyyar CNPP ta bayyana cewa gazawar Kyari na magance wadannan matsalolin ya sa bai dace da mukaminsa ba.
Kungiyar ta CNPP ta kuma nuna damuwarta kan yadda ake shigo da man fetur mara inganci, wanda ta ce “yana da matukar hadari ga lafiyar ‘yan Najeriya.”
Hukumar ta soki wasu makudan kudade da aka ware domin gyara matatar mai ta Fatakwal, inda ta bayyana hakan “wata alama ce ta rashin gudanar da aiki da kuma gazawar da ta addabi kamfanin NNPC.
Ƙungiyar CNPP ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya dauki kwakkwaran mataki domin tabbatar da adalci ga ‘yan Nijeriya da kuma rage musu radadi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj