Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roki ƴan Najeriya da su ƙara yin haƙuri da gwamnatinsa, inda ya tabbatar da cewa ƙasar nan na dab da shiga sabon shafi.
Alfijir labarai ta ruwaito shugaba Tinubu yayi riƙon ne a ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa yasan ƴan Najeriya na cikin matsi sakamakon janye tallafin man.
“Ƴan uwa ƴan Najeriya, wannan lokaci zai zama mai wuya gare mu, babu makawa muna cikin yanayi na wahala amma ina buƙatar mu yi hakuri da wannan yanayi na wucin gadi. Dukkan tsare tsarenmu masu kyau suna aiki. Mafi muhimmanci shi ne nasan zasu yi aiki.”
Shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa matakan da gwamnatinsa take ɗauka zai fitar da kasar nan daga matsin tattalin arziki, inda ya bukaci yan Najeriya da su mika yardarsu ga gwamnatinsa.
“Ina rokon ku, ku mika yardarku kan kokarinmu na sauke nauyi kuma mun damu da walwalar mu”.
Tinubu ya kuma jadadda kudurinsa na bayar damar samun ilimi ga yan Najeriya ta hanyar fito da tsarin bashin karatu ga dalibai.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj