Daga Aminu Bala Madobi
Akalla mutane uku ne suka mutu yayin da 7 suka samu raunuka bayan da wani gini ya rufta sakamakon mamakon ruwan sama a karamar hukumar Nangere da ke jihar Yobe.
Alfijir labarai ta ruwaito lamarin ya faru ne a Tsohon Gari da ke hedikwatar karamar Hukumar Nangere a karshen makon nan.
An tattaro cewa ruwan ya lalata gidaje sama da 50, lamarin da ya sa iyalai da dama suka rasa matsuguni.
Shuwa Adamu, wani mazaunin al’ummar ya shaida wa Daily Trust cewa ruwan saman ya zo kamar da bakin kwarya kuma da iska mai karfi.
“Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9 na safe lokacin da mazauna garin da dama ke shirin fara kasuwancinsu na yau da kullum.”
“Akalla shaguna da gidaje 50 ne suka rushe sannan kuma an rasa ran wani yaro dan shekara bakwai.
Da yake mayar da martani kan ibtila’in, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA) Dakta Goje Muhammad ya jajanta wa wadanda abin ya shafa.
Ya ce hukumar za ta biyan kudaden jinyar duk wadanda suka jikkata a babban asibitin Nangere, inda ya kara da cewa wadanda suka jikkata duk an sallame su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
