Sakamakon wani sako da yake ta yawo a kafafen yada labarai na zamani bisa nadin wani mutum wai shi Amir Umar El Ali a matsayin Sarkin Kutumbawa na kasar Amurka Maigirma Mai Unguwar Kutumbawa yana sanar da Masarautar Kano da dukkan Al’Umma cewa shi bai san wannan mutumin ba, kuma shi bai bayar da iznin a nada shi wannan sarautar ba, hasali ma shi Mai girma Mai Unguwa bai taba ganin sa ba, kuma bashi da hannu a cikin wannan nadin.
A ko ina Kutumbawa suke a fadin duniya Kano ne tushen su, kuma matukar haka ne Mai girma Mai Unguwar Kutumbawan Kano wanda Masarautar Kano ta ke sane da nadin sa da kuma zaman sa shugaban na wannan Al’umma mai albarka ta Kutumbawa, don haka ya kamata dukkan wani nadi ko wani mukami da za a bayar a sanar da shi kuma a nemi izininsa.
Don haka a madadin dukkan al’ummar gidan sarautar Kutumbawa da ahalin su da hakiman sa, Mai Unguwa na nesanta kan sa da na jama’ar sa daga wannan haramtaccen nadin kuma a halin yanzu a na gudanar da bincike domin daukar matakin da ya dace na shari’a a kan dukkan wanda yake ko suke da hannu a cikin wannan badakala.
Allah ya bamu lafiya da zama lafiya
Dokajin Kutumbawan Kano a madadin
Mai Unguwar Kutumbawa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj
