Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Hawan Babbar Sallah A Fadin Jihar Kano Baki Daya

FB IMG 1718219427813

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta ce ta haramta hawan sallar yayin bukukuwan Babbar Sallah a jihar.

Alfijir labarai ta hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu.

Sanarwar ta ce rundunar ta dauki wannan matakin ne sakamakon barazanar tsaro da za a iya samu idan an gudanar da hawan sallar.

” Bayan ganawa da duk masu ruwa da tsaki a jihar kano, Rundunar yan sandan jihar kano ta hana yin duk wani hawa a yayin bikin sallah babbar dake tafe” a cewar Sanarwar.

Rundunar ta ce ta haramta hawan a dukkanin fadin jihar kano baki daya.

Rundunar ta bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar idin su cikin kwanciyar hankali da lumana a inda suke, su kuma cigaba da baiwa rundunar hadin kai don cigaba da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *