Wannan ya biyo bayan muhawarar da aka tafka a zauren Majalisar dokokin jihar dazu dazun nan
An yi la’akari da kudurin dokar gyara masarautun jihar Kano a zauren majalisar bayan kammala karatu na biyu da na uku a safiyar ranar Alhamis.
Tun da farko mataimakin shugaban majalisar Alhaji Muhammad Bello Butu Butu ya bayyana cewa soke dokar zai kara farfado da martabar Kano da aka rasa domin rabon masarautar Kano zuwa biyar ya rage kima da martabar jihar a matakin kasa.
Shugaban masu rinjaye Alhaji Lawan Hussaini Dala ya ce majalisar masarautar ta kasance mai kula da al’adu wanda aka gurbata saboda samar da karin masarautu.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Dala ya bayyana cewa tare da gyara dokar an soke dukkanin masarautun guda biyar yayin da kwamishinan kananan hukumomi zai zama mai kula da su.
Majalisar ta kuma amince da kudirin kafa sabuwar masarauta mai daraja ta biyu a jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl