Sarkin Kano Ya Magantu Kan Matan Yan Sanda Yayin Wata Ziyara Da Suka Kai Masa

IMG 20240516 WA0137

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR.JP  ya bukaci kungiyoyin matan yan sandan kasar nan dasu kara himma wajen hada kan kungiyar matan yan sandan domin koyawa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kansu.

Alfijir labarai ta rawaito mai Martaba ya bulaci hakan ne lokacin da kungiyar Matan yan sandan jihar kano Police Officers Wives Association suka kawo masa ziyara a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace yaji dadin wannan ziyara da kungiya  Matan yan sanda suka kawo masa tareda kudiurin da suke dashi na taimakawa marayu don su dogara da Kansu ba sai gwamnati ta basu aikin yi ba.

A nata jawabin Shugabar Kungiyar kuma Matar Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Hajiya Aisha Muhd Hussain Gumel tace tazo fadar Sarkin ne domin nuna goyon bayanta ga masarauta da kuma basu shawarwari domin cigaba kungiyarsu.

A wani cigaban kuma Mai Martaba sarkin na Kano ya kai ziyara asibitin Murtala fake cikin birnin Kano domin duba marasa lafiya  wadanda wani matasa ya bankawa wuta a massalaci a dai dai lokacin da suke gabatar da sallar asuba garin gadam dake Larabar Abasawa a karamar hukumar gezawa.

Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan nuna jimami da alhinin abunda ya faru yayi addu’ar fatan samun lafiya a garesu da kiyayewar afkuwar hakan.

Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu yasa aljanna madaukakiya itace makoma a garesu.

Sa hannu Abubakar Balarabe Kofar Naisa Press Secretary Kano Emirate Council.
16/5/2024

IMG 20240516 WA0056
PRO
IMG 20240516 WA0139
PRO
IMG 20240516 WA0140
PRO

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *