Labari Mai Dadi! Kakakin Majalisar Dokoki Zai Aurar Da Mata Marayu Guda 100

IMG 20240511 WA0088

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, ya bayyana shirin aurar da wasu marayu mata 100 da suka rasa iyayensu sakamakon harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Mariga.

Alfijir labarai ta rawaito Sarkindaji ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Shugaban majalisar ya yi alkawarin biyan sadaki tare da sayo duk wasu kayan da ake bukata don daurin auren.

Hakan tasa aka zabo ‘yan matan da za a aurar da su cikin tsanaki daga cikin ‘yan mata 170 da aka mika sunayensu.

Shugaban wanda ke wakiltar mazabar Mariga, ya bayyana shirin a matsayin wani shiri na karfafawa mazabarsa da nufin rage radadin talauci.

Ya kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umar Bago da Sarkin Kontagora Alhaji Mohammed Barau za su kasance masu kula da marayun matan a yayin daurin auren gama gari.

Ana sa ran babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, zai halarci taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Mayu a Bangi, hedkwatar karamar hukumar Mariga.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *