Daga Aminu Bala Madobi
Bayan fitar rahotannin sabon tsarin biyan kudin tallafin tsaro da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan fannin tsaro Mal. Nuhu ribado ya fitar.
Alfijir labarai ta rawaito yanzu bayanai sun nuna cewa za a fara tatsar ‘yan Najeriya kudade daga irin yadda suke tasarrafi da musayar kudade kamar haka
Ga bayanan dalla-dalla kan kudin da za a rika turawa ofishin Mallam Nuhu Ribadu (NSA)
Kudin tallafin tsaro (Cyber security levy) :
Daga yanzu kenan za a caji duk wani mazaunin Najeriya kudade tallafin tsaro kamar haka
Za a dauki ₦5 akan kowacce ₦1,000 da ka tura.
₦50 idan kayi muamala ko tura kudi da yakai ₦10,000
₦500 idan kayi amfani wajen tura ₦100,000.
₦5,000 idan kayi cinikayya ko ka tura kudi da yakai ₦1,000,000.
Sannan kuma za a caji mutum kudi dayakai ₦50,000 idan ka tura kudi da yakai ₦10,000,000
Kudin STAMP DUTY: Wanda aka tura masa.
₦50 akan kowacce ₦10,000
₦50 akan kowacce ₦100,000
₦50 akan kowacce ₦1,000,000
₦50 akan kowacce ₦10,000,000
Cajin kudin tura kudi ta USSD ko ta bankuna:
Za a dauki ₦10 idan ka tura kudi kasa da ₦5,000
Za adauki ₦25 idan kayi kokarin tura kudi daga ₦5,001 —zuwa ₦50,000
Sannan za a caji mutum ₦50 idan ya tura kudi sama da ₦50,000
Kudin Harajin VAT: Mai tura kudi…
Za a caji mutum ₦0.75 akan tura ₦10, yayin da za a dauki ₦1.875 akan tura ₦25 sannan kuma ₦3.75 idan aka tura ₦50
Kudin tura sakonni: Mai tura sako da wanda ya karbi sakon duk za a caje su ₦4 a kowanne irin sako dasuka tura.
Wannan lamari zai shafi kowanne irin bangare na harkokin tasarrafin kudade
A duk musayar kudi da ‘yan kasa zasuyi misali da ta kai Naira 1m, to za’a cire 5K kenan, idan a wata dan kasuwa yana juya kudade tareda tasarrafi dash wajan tura su zuwa wani waje na daban za arika dauka wani kaso cikin adadin yawan kudin da yayi muamala dasu.
Idan mutum ko dan kasuwa yayi muamalar kudi da ta kai Naira 50m, to za a cire masa Dubu 250.
A shekara kenan za’a cire masa 3million.
Ga kuma fannoni 15 na hada-hadar kudade a bankuna wanda ba za a cire ko da 0.5% ba
1. Karban bashi da kuma biyan bashi.
2. Biyan albashi
3.Tura kudade ta bankuna iri daya kokuma mabanbanta ga mutum me banki iri daya.
4. Canje-canje a cikin banki tsakanin abokan ciniki na banki ɗaya
5. Musayar kudade ga Cibiyoyin Kuɗi zuwa ga bankunan wakilan su
6. Musayar kudade tdaksnin banki da banki iri guda dake gurare daban daban
7. Canja wurin zaman kudade na bankuna zuwa CBN.
8. Canje-canjen kudade a reshe cikin banki
9. Wasiƙun Ƙira
10. Kudaden da ke da alaƙa maido da kudaden jari-hujja da motsin kuɗi mai yawa daga asusun kudi
11. Ajiyar kuɗi, gami da ma’amaloli da suka haɗa da zuba jari na dogon lokaci kamar Takaddun Kuɗi, Lamuni, da Takardun Kasuwanci.
12. Tsare tsaren samar da walwala da jin dadin Jama’a na Gwamnati misali; Biyan fansho
13. Mu’amalar da ba ta da riba, gami da ba da gudummawa ga ƙungiyoyi masu zaman kansu ko ƙungiyoyin agaji masu rijista.
14. Mu’amalar cibiyoyin ilimi, gami da biyan kuɗin koyarwa da sauran ma’amaloli da suka shafi makarantu, jami’o’i, ko sauran cibiyoyin ilimi.
15. Ma’amaloli da suka shafi asusun ajiyar banki kamar asusun dakatarwa, share asusun ajiya, asusun riba da dai sauransu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl