Kumfayakun! Yadda Mai Sayar da Kankara da ya mallaki gidajen mai 120, motocin dako 600 A Najeriya

IMG 20240503 WA0026

Daga Aminu Bala Madobi

Alh Auwalu wanda aka fi sani da A.A Rano, ya rikide daga mai gudanar da karamar Sana’a a kauyen Kano zuwa hamshakin attajiri a Nigeria, inda ya mallaki wani kamfani da yake da gidajen mai guda 200 a fadin Najeriya.

Alfijir Labarai ta rawaito A A Rano, haifaffen garin Lausu ne dake karamar hukumar Rano a jihar Kano, ya fara harkokin kasuwanci da sana’ar kankara da man gyada, gami da sauran kayayyakin Amfanin gida na yau da Kullum.

Alhaji Auwalu Rano ya fara gina wani kamfani na biliyoyin naira wanda ya shafi sassa daban-daban na tattalin arziki a Najeriya.

A yanzu, A A Rano ya mallaki kamfanin AA Rano oil & Gas, tare da depo na tankunan dake cin liter mai miliyan 56 a Legas, sannan ya mallaki manyan motocin dakon mai guda 600 , kuma yana da gidajen Mai kimanin 120 a duk faɗin Najeriya da fiye da 600 da kuma jirgin ruwa karkashin kamfanin MT LAUSAU.

Hakazalika AA Rano yana da Kamfanoni da Suka hadar da RanoGaz, Wanda yake kula da harkokin man fetur da Iskar Gas, kamfanin sarrafa shinkafa, sai Rano Lubricant, da Rano Air, Lausu Marine and Logistics, AA Rano Terminal, da AA Rano Road Haulage.

IMG 20240503 WA0027 1
A A Rano

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *