Labari Mai Dadi! Dubun Wani Mai Garkuwa Da Mutane Ta Cika

Screenshot 20240502 152937 Facebook

An kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Abubakar Ali Damina mai shekaru 43 a kauyen Ofodo da ke kusa da garin Egabada a karamar hukumar Igalamela-Odolu ta jihar Kogi.

Alfijir Labarai ta rawaito wanda ake zargin, dan asalin karamar hukumar Bida ta jihar Neja, an kama shi ne a ranar Litinin a wani samame da jami’an tsaro da ƴan banga suka gudanar, inda aka same shi da bindiga kirar gida tare da wasu abubuwa da ake tuhuma da suka hada da layu, da harsasai na gida.

Kwamandan ƴan banga a yankin, Mohammed Ajitata ya ce Damina, wanda ya amsa laifin ya yi zargin cewa wani mutum dan kauyen Shanawa da ke karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi, abokin aikata laifin sa ne.

Ajitata ya ci gaba da cewa, “Muna kan bin sa ne tun lokacin da muka gano laifukan da ya aikata a unguwar Egabada-Odolu. A ranar Litinin din da ta gabata ne wani rahoton sirri ya bayyana maboyar sa kuma mun sanar da jami’an tsaro lamarin da ya kai ga cafke shi a wani samame na hadin gwiwa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Aya, wanda aka tuntube shi a kan lamarin ta hanyar sakon kar ta kwana da kiran waya, bai bada amsa ba.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *