Wata motar fasinja da ta taso daga Bauchi ta yi hatsari a Enugu kuma mutum 16 daga cikin fasinjoji 18 dake motar maza 14 mata 2 sun mųțtu, wasun su ma ba a iya gane su don sun ƙ0ne ƙurmus.
Alfijir Labarai ta ruwaito Yan sanda sun ce lamarin ya faru da yammacin jiya Talata, 30 ga watan Afrilu a babban titin garin Ekwegbe.
Motar ƙirar Toyota Hummer Bus ce 18 seater dauke da lambar Bauchi, DAS 215 XA, kuma an rubuta “Masha Allah” a jikin motar.
Don haka Kwamishinan yan sanda na Enugu ke roƙon jama’a duk wanda Allah yasa ya san wani daga cikin fasinjojin to a tuntubi rundunar a 08098880172 ko 08086671202

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇