Tirka-Tirka! Wasu Matasa Sun Garkame Wani Masallacin Juma’a a Kano

IMG 20230923 WA0013

Daurawan matasa a garin Kwagwar dake Karamar Hukumar Gezawa sun rufe babban Masallacin garin tare da hana Sabon Limamin Garin Jan Sallar Juma’a saboda zargin rashin cancantarsa .

Alfijir labarai ta rawaito makon da ya gabata ne Alumar garin na Jama’ar Kwagwar suka zargi Dagacinsu da Hakimin Gezawa da Masarautar Gaya da Kuma Baturen Yan Sanda na Gezawa DPO da kakabawa Al’ummar garin sabon limamin da basa so saboda zargin rashin cancantarsa wato Malam Ibrahim Audu.

Nasara Radio ta wallafa cewar Dattawa da matasan garin sunyi zargin amfani da Kudi wajen nadin sabon limamamin daga Dagacin Garin zuwa fadar Hakimin Gezawa har zuwa fadar Masarautar Gaya .

Bayan mutuwar tsohon Limamamin Malam Aminu Ma’aruf sai Hakimin Gezawa ya nada Dansa Malam Tajudden Aminu Amma daga baya Hakimin ya warware nadin nasa aka nada wani daban saboda zargin bada cin hanci .

Tuni dai matasan garin na Jama’ar Kwagwar suka sake shirya zanga zanga tare da rufe duk wata hanya ta shiga Masallacin wanda haka yasa ba,ayi sallar Juma’a a Masallacin ba a Karon farko.

Haka kowa ya hakura ya koma gida ciki harda sabon limamamin wasu kuma sukaje masallaci mafi kusa dasu.

Nasara Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *