Gwamnan jihar Bauchi, Sen Bala Mohammed, ya amince da karin rabin kudin aikin Hajji na Shekarar 2024 ga maniyyatan jihar.
Alfijir labarai ta rawaito Hakan na nuni da cewa gwamnatin jihar ta bayar da Tallafin ₦959,000 ga kowane mahajjata 1,652 Daga jihar, wanda ya kai Naira biliyan 2.5.
Kwamishinan al’amuran addini da wayar da kan al’umma na jihar, Alhaji Yakubu Hamza ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Bauchi a Yau Juma’a.
Kwamishinan yace, “wadanda za su amfana da maniyyata sun hada da wadanda suka rigaya sun biya karin kudin da kuma da kuma wadanda Gwamnatin jihar ta ba su gurbin aikin Hajji.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk
