Tawagar Rasha ma ta ziyarci Nijar a watan Disambar da ya gabata.
Alfijir labarai ta rawaito Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya tattauna ta wayar tarho a ranar Talata da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin game da “ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro”, a cewar sanarwar da aka fitar a hukumance.
Tuni dai kasashen biyu suka amince a watan Janairu domin ƙarfafa alaƙar soji a lokacin da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine ya jagoranci wata tawaga zuwa birnin Moscow.
Nijar, ɗaya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, ta kasance kan gaba a hadin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya wajen yaƙar masu tada ƙayar baya a yankin Sahel, amma ta rungumi Rasha a matsayin sabuwar abokiyar tsaro tun bayan hambarar da zababben shugaban kasar a bara.
Shugabanin kasashen biyu “sun yi magana kan buƙatar ƙarfafa hadin gwiwa a fannin tsaro…domin fuskantar barazanar da ake fuskanta a halin yanzu,” in ji sanarwar ta Nijar, wadda aka karanta a gidan rediyon gwamnatin ƙasar.
‘Dabarun haɗin kai’
Har ila yau, sun tattauna “ayyukan don haɗin gwiwar bangarori da dama da na duniya,” in ji sanarwar, ba tare da ba da ƙarin bayani ba kan hakan.
Janar Tchiani, wanda ya jagoranci Nijar tun bayan juyin mulkin watan Yuli, ya gode wa Putin saboda “goyon bayan” da Rasha ke ba kasar ta yankin Sahel da kuma gwagwarmayar neman ‘yancin kan kasa.
Tawagar Rasha ma ta ziyarci Nijar a watan Disambar da ya gabata.
Har yanzu dai dakarun Amurka kusan 1,000 na jibge a Nijar duk da cewa an taƙaita zirga-zirgarsu tun bayan juyin mulkin, kuma Washington ta daƙile tallafin da take bai wa gwamnatin.
Nijar ta ayyana daina alaƙar soji da Ƙasashen Yamma
Wata babbar tawagar Amurka ta je Yamai a tsakiyar watan Maris domin sabunta hulɗa da gwamnatin mulkin soja, amma ta ce ba su gana da Tchiani ba.
Sabuwar gwamnatin ta yi Allah wadai da haɗin gwiwar soji da Ƙasashen Yamma, tare da yin watsi da alakar mulkin mallaka da Faransa.
A baya dai Nijar ta kasance muhimmin sansani ga kokarin sojojin Faransa na murƙushe ta’addancin da ya samo asali daga yankin Sahel.
Nijar ta bi sahun ƙasashen maƙwabta Mali da Burkina Faso a farkon wannan wata wajen sanar da kafa rundunar hadin gwiwa da za ta yaƙi hare-haren ta’addancin da aka daɗe ana fama da su a cikin ƙasashen uku.
A watan Janairu ne dai suka bayyana aniyarsu ta ficewa daga kungiyar ECOWAS daga kungiyar kasashen yankin Yammacin Afirka.
TRT Africa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk
