Ana tsaka da sallar tarawi a yau asabar yan bindiga sun shiga garin Mairua sun kashe babban mutum mai suna Alh Lado Mairua da wani makwabcinsa
Alfijir labarai ta rawaito yan bindiga sun shiga garin Mairua yankin ƙaramar hukumar Faskari, inda suka tunkari gidan Alh Lado Mairua, wanda babban mutum ne kuma shahararre a yankin, in da suka kashe shi suna cikin sallar tarawi tare da wani makwabcinsa mai suna Sani Autan Haris
Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ne ya tabbatar wa Katsina Daily News faruwar lamarin, inda yana magana cikin kuka yana cewa “Sun kashe mun ubana da makwabcinmu”

Yankin ƙaramar hukumar Faskari na daya daga cikin manyan yankuna dake fama da matsalar tsaro a jihar Katsina, inda da wuya a yi kwana ɗaya ba a sami rahoton yan bindiga sun kai hari a wasu garuruwan yankin ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇