Ibtila’i! Gobara Ta Lakume Shaguna 37 A Wata Kasuwa Dake Kano

FB IMG 1709891079107

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar .

Alfijir labarai ta rawaito kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 01:37 na safiyar Laraba.

A cewar Abdullahi, da misalin karfe 01:37 na safe ne wani Malam Baba yayi musu waya cewa gobara ta tashi a kasuwar dake Zuwaciki.

“Mun yi gaggawar tattara jami’an mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 01:47 na safe, muka kashe gobarar domin kada ta bazu zuwa wasu shaguna,” inji shi.

Abdullahi ya ce shagunan 37 sun kasance a kasan bene na wani gini dake kasuwar.

Ya kara da cewa wasu shaguna uku ne gobarar ta dan yi barna.

A cewar sa, ba a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *