EFCC Ta Kwato wa Yan Fansho Gidaje 324 A Jihar Kano

Screenshot 20240319 125014 com.android.chrome edit 2221532438202

Wannan na zuwa ne bayan shafe shekaru masu yawa ana shari’a da bincike.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC shiyyar Abuja ta mika wasu takardun gidaje 324 da aka kwato mallakar ‘yan fanshon jihar Kano,

Alfijir labarai ta rawaito mika gidajen, ya biyo bayan umarnin karshe da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar, biyo bayan nasarar binciken da hukumar ta gudanar kan wani asusun fansho na Naira biliyan 4.1 da ‘yan fansho suka mallaki gidaje.

Rahotanni dai sun bayyana cewa wasu gwamnatoci biyu da suka gabata a jihar Kano sune suka handame su.

Hukumar ta binciki wani koke da ma’aikata da ‘yan fansho na jihar Kano suka shigar kan zargin karkatar da kudaden fansho a jihar.

Binciken da hukumar EFCC ta gudanar ya nuna cewa gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniya da asusun fansho na jihar Kano na kashi uku na gina gidaje a kan jimillar kudi naira biliyan 4.1, wanda asusun fansho zai ba da gudummawa.

Yayin da yake mika takardun kadarorin 324 na Naira biliyan 4.1 ga ‘yan fansho, kwamandan hukumar ta EFCC na shiyyar Abuja, mataimakin kwamandan EFCC, Adeniyi Adebayo, ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta na ganin ta kawar da a ayyukan zamba.

Wakilan Hukumar Fansho ta Jihar Kano, Alhaji Hassan Muhammed Aminu, da Kubra Ahmad Bichi da Salisu Yakubu Abubakar, wadanda suka karbi takardun a madadin ma’aikata da ‘yan fansho, sun bayyana jin dadinsu da hukumar EFCC ta taimaka musu wajen kwato gidajen nasu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *